Iran: An Nada Sabbin Kwamandojin Rundunar “Khatamul-Anbiya” Na Tsaron Sararin Samaniya

A karkashin umarnin babban kwamandan rundunar sojan kasar Iran, an nada sabbin kwamandojojin rundunonin hadin gwiwa na tsaron sararin samaniya na “Khatamul-Anbiya” tare da sojojin kasa. An nada Laftanar kasar Ali Ridha Ilhami a matsayin babban kwamandan rundunar “Khatamul-Anbiya” ta tsaron sama, da kuma cibiyar hadin kai ta tsaron sararin samaniya da sojojin kasa. Shi […]

Kasashen Nigeria Da Iran Za Su Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Makamashi

Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Iran sun jaddada azamarsu ta ganin bunkasa alakarsu a fagagen kasuwanci, zuba hannun jari, makamashi bayan da su ka yi wata tattaunawa a birnin Abuja. An yi tattaunawar ne a jiya 17 Disamba a ginin ma’aikatar harkokin waje dake Abuja,a tsakanin Dunoma Ahmed wanda shi ne babban satakaren ma’aikatar, da […]

Iran Ta Gargadi Amurka Kada Ta yi Amfani Da Tattaunawa Don Raunan Iran Kan Isra’ila

Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Tehran ba za ta taba amincewa da sharuddan kasantarwa ba don tattaunawa da Amurka, yana gargadi game yunkurin kwace karfin sojan iran da kuma raunanta akan gwamnatin Isra’ila. Da yake Magana da manyan jami’an gwamantin da manyan yan siyasa a jiya laraba prezeshkiyan yace: iran ta tattaunawa […]

Falasdinawa 17 Ne Suka Mutu A Gaza Saboda Tsananin Sanyi

Rahotanni sun bayyana cewa yanayin sanyi mai tsanani da aka shiga a yankin gaza yayi sanadiyar mutuwar falasdinawa da dama,a cikin wannan watan kamar yadda majiyoyin labaran yankin suka bayyana, adadai lokacin da Isra’ila take ci gaba da hana shigar da kayayyakin agaji da suka hada da Haimomi da sauran abubuwan bukatun rayuwa na yau […]

Iran da Rasha Sun yi Watsi Da Kasancewar Sojojin Ketare A Yankin Kafkaz

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a yayin tattaunawarsa da takwaransa na kasar Rasha ya bayyana cewa tabbatar da tsaro a kafkaz da tsakiyar Asiya ya doru ne a wuyan kasashen yankin, don haka basu yarda wani daga wajen ya tsoma baki cikin harkokinsu ba. Yankin Kafkas ya zama cibiyar gasar siyasa a tsakanin […]

Jam’ian Yan Sanda A Birtaniya Sun Kama Wasu Masu Rajin Kare Hakkin Falasdinu Guda 11

Rahotanni sun bayyana cewa jamian yan sandan Birtaniya sun kama mutane 11 masu nuna goyon bayan alummar falasdinu a garuruwa daban-daban na kasar bayan da suka rera taken intifada a lokacin zanga-zanga, wanda haka ke nuna irin yadda ake take hakkin bayyana albarkacin bakin. Haramcin furta kalma guda acikin jamaa a lokacin zanga-zanga yana sanya […]

Maduro : shirin Amurka na mayar da Venezuela karkashin ikonta ba zai taba tabbata ba

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ce kalaman Shugaban Amurka Donald Trump game da “kwato” filaye da mai na Venezuela ya fallasa ainihin manufar Amurka, yayin da yake tabbatar da cewa Washington ba za ta “taɓa” mayar da ƙasar Latin Amurka ta zama “mallakarta ba.” Da yake jawabi a wani gangami a Caracas ranar Laraba, Maduro […]

Iran da Rasha sun karfafa dangantaka a tsakaninsu

Kasashen Iran da Rasha sun cimma yarjejeniyoyi da dama a tsakaninsu na karfafa dangantaka. An bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na hadin guiwa tsakanin Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Rasha, Sergey Lavrov, . Manyan batutuwan da aka tattauna sun hada da dangantakar kasashen biyu, hadin gwiwar tattalin arziki, takunkumin […]

Trump ya hana ‘yan Nijar, Burkina da Mali shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗaɗa dokar hana tafiye-tafiye don dakatar da shiga kasar ga karin wasu kasashe biyar na Afirka. Wannan sabon mataki ya shafi masu fasfo daga Burkina Faso, Mali, Nijar, Sudan ta Kudu, da kuma Saliyo. Sabon matakan, zai fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026. Ga Burkina Faso, Mali, da […]

MDD : An Kashe ‘Yan Jarida 289 Tare da Kama Sama da 200 a Gaza

Majalisar Dinklin Duniya ta yi gargadi game da yawan ‘yan jaridan da aka kashe a zirin Gaza, yayin da kuma aka kama sama da 200. Tsakanin watan Oktoba 2023 zuwa tsakiyar watan Disamba 2025, ‘yan jarida 289 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila a Gaza, in ji Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na […]

Iran ta yi tir da Amurka kan haramta fitar da man fetur din Venezuela

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta fitar da wata sanarwa tana mai Allah Wadai da barazanar Amurka na sanya takunkumin hana safarar man fetur din Venezuela tana mai danganta matakin da marar ma’ana. Iran ta bayyana matakin a matsayin wata alama ta cin zarafi da amfani da karfi,” wadda ya zama keta dokokin kasa da kasa, […]