Iran Ta Yi Tir Da Abinda Amurka Take Yi A Kasar Cuba

Ministan harkokin wajen kasar Iran ABbas Araci ya yi tir da gwamnatin kasar Amurka kan killace kasar Cuba da take yi watanni da suka gabata,

Ministan harkokin wajen kasar Iran ABbas Araci ya yi tir da gwamnatin kasar Amurka kan killace kasar Cuba da take yi watanni da suka gabata, da kuma takurawa mutane da jami’ar kasar ta take yi.

Tashar talabijan ta Presstv a nan tehran ta nakalto argchi yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa, takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar Cuba shekaru kimani 70 da suka gabata sun sabawa dokokin kasa da kasa.

Ya kira sammashin da gwamnatin Amurka ta fitar a shekarun baya tare da umurni ga gwamnatin jihar Florida ta kama shugaban kasar Cuba Raul Castro a matsayin wanda baya bisa doka kuma ya sabwa diyaucin kasar. Faransa Ta Tsawaita Lokacin hana fita a wasu yankuna a Kasar.

Gwamnatin kasar Faransa ta tsawaita doka harna fita wacce aka kafa a wasu garuruwa akasar kafin gagarumin zanga zanga wacce mutanen kasar suka shirya zasu gudanar a ranar asabar mai zuwa.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sébastien Lecornu firay ministan kasar yana cewa sun tsawaita dokan hana fita dare a birnin Paris babba birnin kasar da wasu garuruwa. Sannan zasu kara yawan jami’an tsaro a kan titunan wadanna n birane tare da sojoji a wannan karon.

Haka ma ministan cikin gina na ksar ya kara jadda wannan umurnin ya kuma kara da cewa a wannan karon zasu yi amfani da sojojin kasar don murkushe duk wani gangamin da za’a gudanar a ranar asabar mai zuwa.

A wani labarin kuma kungiyar taliban jami’o’I a kasar UNEF ta bayyaa cewa daliban kungiyar zasu fito kan tituna a ranar asabar mai zuwa don takurwa shugaba Macron kan canza tsarin kula da ilmi a kasar don kyautata shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted