Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Baka’i ya yaba da hikimar shugabannin kasashen biyu da su ka dakatar da yaki, yana kuma nuna fatansa na ganin kasashen biyu sun mayar da alakarsu kamar yadda take a baya a cikin gaggawa.
A jiya Asabar ne dai ministocin harkokin wajen kasashen biyu su ka sanar da tsagaita wutar yaki,bayan kwanaki da su ka dauka suna musayar wuta a tsakaninsu.