Iran Ta Yi Kira Ga MDD Ta yi Watsi Da Takunkumin Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi yayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin dunniya da dukkan mambobinta da su yi watsi da takunkumin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi yayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin dunniya da dukkan mambobinta da su yi watsi da takunkumin tattalin arziki da kasar Amurka ta kakaba mata, yace Amurka tana son ta tilastawa sauran kasashen barin kyakkyawar dangntakar tattalin arziki dake tsakaninsu da Tehran ta hanyar barazanar kakaba musu takunkumi

Acikin wata wasika da ya aikewa babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Gutteres kuma shugaban kwamitin tsaro da dukkan mambobin mjalisar ajiya laraba  babban jami’in diflomasiyar ya bayyanan cewa mataken da Amurka ta sanar a baya bayan nan karkashin abin da kira da Operation economic expulsion yaya kama da yukunrin kakabawa kasashe masu yanci manufofin amurka da karfin tsiya.

Araqchi ya kirayi majalisar dinkin duniya ta tayi tir da wannnn mataki kuma tayi watsi da shi  ko kuma ta hana yin aiki da shi,kuma ta matsawa Amurka ta kawo karshen wannan barazana da mummunan matakin kan sauran kasashen da suka ci gaba da huldar kasuwancinsu da kasar iran

Daga karshe ya caccaki Amurka game da harin fararen hula da take yi da gangan yace wannan matakin an tsara shi ne ta yadda za su kaucewa kariyar da ake bawa fararen hula a karkashin dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted