Iran Ta yi Kira Ga Kasashen SCO D su Kalubalanci Amurka

iran ta yi kira ga kasashen SCO da su kalubalanci ta'addancin amurka da isra'ila

Babban mai shigar da kara na kasar iran Janar  mohammad Mavahedi-azadi yayi kira da a kafa kwamiti tsakanin kasashen kungiyar hadin guiwa ta shanghai da su haka kansu wajen tunkarar ta’addancin kasa da kasa,

Da yake Magana a wajen taro karo na 24 na kungiyar hadin kan kasahen shangai a kazan na kasar Rasha a yau alhamis Mavahedi-Azad yayi kira da a kafa kungiyar kasa da kasa don yin aiki tare domin kare hare haren da ake  kai wa kan fararen hula da kuma yara kana a kasar iran

Yace ya kamata duniya ta fahimci cewa wadanda suke zubar da jinin yara yan makaranta a kasar iran ba za su taba neman a kare hakkin yara kanana da jaririrai ba

Babban mai shigar da karan na kasar iran ya gana da takwaransa na kasar rasha a gefen taron na kazan, kuma sun sanya hannu kan yarjejeniyar hadin guiwa tsakanin kasashen biyu,

 Ita dai kungiyar SCO an kafa ta ne a shekara ta 2001 kuma tana da mambobi 10 da suka kunshi kasashen Rasha ,Indiya, Kazakhastan, Kyrgystan, TajikistanTajikistan, uzebekistan da kuma kasar balarus

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted