Kungiyar kwallon kafa ta Iran ta aike da sako zuwa ga hukumar kwallon kafa ta duniya da ta kori HKI daga cikinta
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Iran Mahdi Taj, ya bayyana cewa: Mun yi kira ga Sheikh Salman akan daukar kwakkwaran mataki akan ‘Yan Sahayoniya. Mun kuma rubuta wasika zuwa ga Fifa akan cewa ya zama wajibi a dagawa HKI jan kati.
Bugu da kari, ya kuma ce; “Yan sahayoniya sun kai wa hukumar kwallon kafa ta Iran hari, ta kuma kashe mana alkalai, ‘yan wasa, don haka ya zama wajibi a kore su daga Fifa.
Taj ya kuma ce; Mun sami ci gaba sosai a wannan fagen, muna fatan kungiyar Fifa ta yi la’akari da wadannan laifukan na Isra’ila.