Iran ta yi kakkausar suka kan sabon takunkumin Amurka

Iran ta yi kakkausar suka kan sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Ministan Man Fetur na aksar Mohsen Paknejad da wasu hukumomi da jiragen ruwa

Iran ta yi kakkausar suka kan sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Ministan Man Fetur na aksar Mohsen Paknejad da wasu hukumomi da jiragen ruwa masu ruwa da tsaki a harkar danyen man fetur da kasar ke fitarwa, tana mai cewa matakin keta doka da munafunci ne daga bangaren Amurka.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baghaei ne ya bayyana hakan yau Juma’a, kwana guda bayan da ma’aikatar baitul malin Amurka ta kakaba takunkumi kan ministan man fetur na kasar Paknejad da wasu kamfanoni uku da ke da hannu a cinikin man Iran a kasar Sin.

Mista Baghaei ya ce, sabbin takunkumin sun karyata ikirarin da jami’an Amurka suke yi kan aniyarsu ta yin shawarwari tare da Iran.

Ya kara da cewa, munanan ayyukan da Amurka ta yi da nufin kawo cikas ga mu’amalar tattalin arziki da cinikayya da Iran da sauran kasashen duniya, ya zama keta dokokin kasa da kasa da cinikayya cikin ‘yanci.

Kakakin ya kara da cewa, matakin da Amurka ta dauka na na sanya wa ministan man fetur na kasar takunkumi, ba zai iya yin wani tasiri ga kudurin kasa na kare ‘yancin kai da martabar kasar da kuma kokarin samar da ci gabanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments