Iran ta yi watsi da sanarwar hadin gwiwa da kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf (GCC) da EU suka fitar tare da jaddada ikonta a kan tsibiran tekun Fasha nan guda uku: Greater Tonb, Lesser Tonb, da Abu Musa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai a wata sanarwa da ya fitar ya yi Allah wadai da tsoma bakin kasashen turai kan lamarin.
M.Baghai ya yi watsi da shishigin na kasashen turan da ya danganta da marar tushe da aka yi a cikin sanarwar hadin gwiwa na taron ministocin harkokin wajen kasashen yankin Gulf na Farisa (GCC) da kungiyar Tarayyar Turai, wanda ya ce wabi yunkuri na haifar da rarrabuwar kawuna da wasu kasashen Turai ke yi a yankin Gulf na Farisa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya sake tabbatar da ikon mallakar tsibirin na dindindin, yana mai jaddada cewa wani bangare ne na kasar Iran.
Tsibirin Abu Musa, Greater Tonb, da Lesser Tonb, dake cikin Tekun Fasha, a tarihi sun kasance wani yanki na kasar Iran, kamar yadda bayanai na tarihi, na shari’a, suka tabbatar a Iran da sauran wurare.
Tsibiran sun kasance karkashin ikon Birtaniya a shekara ta 1921, amma a ranar 30 ga Nuwamba, 1971, kwana guda bayan ficewar sojojin Birtaniya daga yankin, kuma kwanaki biyu kafin Hadaddiyar Daular Larabawa ta zama kasa, Iran ta karbi ikon mallakar tsibirin.
Jami’in diflomasiyyar na Iran ya shawarci makwabtan da ke gabar tekun kudancin tekun Fasha da su mai da hankali kan karfafa zumunci a tsakanin kasashen yankin.