Iran Ta yi Barazanar Janye Ofishin Jakadancinta Dake Birtaniya Saboda Matsalar Tsaro

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi yayi tir da harin da aka kai a baya bayan nan a ofishin jakadancin iran a birnin London,

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi yayi tir da harin da aka kai a baya bayan nan a ofishin jakadancin iran a birnin London, lokacin da wasu masu adawa da kasar iran suka ci zarafin tutar kasar.

A wata tattaunawa da yayi ta wayar tarho da takwararsa ta kasar birtaniya Yvette Cooper, Araqchi ya jaddada cewa bisa dokokin kasa da kasa hakkin birtaniya ne ta bada kariya da tabbatar da tsaro ga offishin jakadancin Iran dake birnin London.

Haka zalika ministan yayi barazanar cewa idan kasar birtaniya ba za ta iya aiki da nauyin dake kanta na tsare ofisoshin jakadanci ba to iran ba ta da wani zabi in banda ta janye jami’anta daga wajen,

Araqchi yayi kira ga birtaniya da ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidan iran , kuma ta dauki mataki kan yan ta’adda da Isra’ila ke marawa baya kamar kafafen yada labarai dake aiki daga birtaniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted