Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Dr. Isma’ila Baka’i, ta yi tir da sabbin hare-haren da HKI ta kai wa kasar Lebanon a daidai lokacin da ake bikin ranar Kudus.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar ta Iran ya bayyana cewa; Abinda HKI ta yi keta tsagaita wutar yaki ne,wanda abin a yi tir da shi ne.
Haka nan kuma ya yi ishara da nauyin da ya rataya akan wuyan Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kasashen da suke cikin sa-ido da ‘yarjeneniyar tsagaita wutar yaki, haka nan kuma ya yi kira zuwa ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki mataki na gaggawa domin kawo karshen maimaita keta tsagaita wutar yaki da ‘yan sahayoniyar suke yi.
Har ila yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce; “ Dalilin da ‘yan sahayoniya su ka bijiro da shi na kai wa Lebanon hari,ba zai zama karbabbe ba, don haka wajibi ne ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki matakin yadda ‘yan sahayoniyar suke keta wutar yaki a cikin Gaza, Lebanon da kuma Syria.
Dr. Baka’i ya bayyana abinda HKI take yi da cewa, baraza ce ga zaman lafiya da sulhu na duniya.
Tun bayan tsagaiwa wutar yaki a kasar Lebanon, HKI tana keta ta a duk lokacin da ta so, kamar kuma yadda ta kafa sansanoni biyar da ta girke sojojinta a ciki.