Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi tir da harin da HKI ta kai wa kasar Syria wanda ya yi sanadiyyar mutuwar gwamman fararen hula.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran din Isma’ila Baka’i yana bayyana damuwarsa a kan fadan da aka yi a yankin Suwaida dake kudancin Syria wanda ya ci rayukan mutane masu yawa.
Haka nan kuma ya yi tir da hare-haren HKI a cikin kwanaki biyu a jere.
Fadan banagranci dai ya barke a yankin Suwaida a tsakanin salafawa da ‘yan Duruz, da ya kai ga mutuwar mutane fiye da 100.
HKI ta shiga cikin fadan da zummar kare ‘yan Duruz daga hare-haren jami’an tsaron gwamnatin Syria.
“Yan sahayoniya da suke fama da karancin sojoji suna son jawo hankalin ‘yan Duruz ne domin su rika shiga cikin sojojinta, lamarin da jagororinsu su ka ki amincewa da shi.