Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya yi allawadai da hare haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wata makarantar hukumar bada agaji ta MDD a Palasdinawa UNRWA atakaice.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ta nakalto Ka’ani yana fadar haka a shafinsa na X a jiya da yamma, ya kuma kara da cewa ta’asan da sojojin HKI suke aikatawa a Gaza su ne zasu zama sanadiyyar rushewarta nan gaba.
A jiya Lahadi ce jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan wata makarantar UNRWA a gaza inda mutane 12 suka kai ga shahada a yayinda wasu kimani 70 suka ji rauni. Sannan akwai yiyuwar karuwar yawan wadanda suka rayukansu sanadiyyar munin raunukan da wasu daga cikinsu suka ji a wadannan hare hare.
Daga karshen Kan’ani ya kammala da cewa kasashen yamma sun yi shiru da bakunansu dangane da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a gaza, don haka suna da hannu a cikin kisan kiyashin da HKI take yi a Gaza.