Iran Ta Yi Allawadai Da Ci Gaba Da Aikata Laifuka Da HKI Take Yi A Gaza

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka,i ya bayyana yadda HKI take ci gaba da kara tafka laifuka a Gaza da

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka,i ya bayyana yadda HKI take ci gaba da kara tafka laifuka a Gaza da a bayan nan su ka kashe mutane 100 a cikin sa’o’i 24.

Har ila yau kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya yi tir da kisan da ‘yan sahayoniyar su ka yi wa dan majalisar dokokin Falasdinu Muhammad Faraj al-Gul da kuma fitaccen mai karatun alkur’ani mai girma Alaa Azzam da kuma iyalansa.

Haka nan kuma kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce, ci gaba da killace yankin Gaza da hana mutane abinci da magani da jefa su cikin yunwa sannan kuma a lokaci daya da kai wa sansanoninsu na zaman hijira hare-hare, wani salon yaki ne na dabbanci akan al’umma domin karar da su, bisa salo irin na mulkin mallaka.

Danagne da cibiyoyin agaji na bogi da Amurka da HKI su ka kafa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce, wadannan cibiyoyin ba komai ba ne sai mafarautar kashe Falasdinawa da yunwa da kishiruwa su ka ci dununsu.

Baka’i ya kuma jaddada cewa rashin daukar mataki akan laifukan ‘yan sahayoniyar ne,ya taka rawa wajen raunana dokokin kasa da kasa ta fuska mafi muni.

Akan masu goyon bayan ‘yan sahayoniya kuwa da su ne Amurka,Jamus da Birtaniya, mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musuluncin ta Iran ya ce, ummul haba’isin da  su ka karfafa ‘yan sahayoniyar suna ci gaba da yaki.

A karshe Baka’i ya yi kira ga kasashen wannan yankin da na musulmi da su dauki matakan da su ka dace domin dakatar da wannan kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted