Iran ta yi tir da Allah-wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta lafta mata.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce matakin wata babbar alama ce da ke nuna cewa Washington ba ta da kyakyawar niyya, hasali ba abar yarda ce ba.
Sanarwar ta bayyana karara cewa Iran ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen matsin lamba na Amurka kuma ta dage kan yin shawarwari a karkashin sharudda guda.
Iran na cewa takunkuman da Amurka ke bayyanawa da matsin lamba mafi girma, tun zuwa gwamnatin Trump, ba zasu tankwaso Tehran ba game da hakokkinta.
Kalaman na zuwa ne jim kadan bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya sanar da kakaba wasu sabbin takunkumi kan hukumomi bakwai da jiragen ruwa guda biyu bisa zargin suna da hannu a cinikin man fetur na Iran.
Matakin na zuwa ne jim kadan bayan Iran ta sanar da cewa za a sake gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da Amurka a birnin Rome a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a karkashin jagorancin kasar Oman.