Kasar Iran ta yi Allah wadai da matakin da majalisar dokokin Canada ta dauka kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci tare da sauran dakarun kasar sune ke da alhakin kare kan iyakokin kasar da tabbatar da tsaron Iran, tare da bayar da gudummawa wajen wanzar da dauwamammiyar tsaro da kwanciyar hankali a yankin ta hanyar yakar mummunar dabi’ar ta’addanci.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya mayar da martani kan matsayin majalisar dokokin kasar Canada na sanya dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda, yana mai kakkausar suka kan wannan mataki da ya bayyana da matakin rashin hikima da kuma nuna kiyayya wanda ya saba wa ka’idoji da kuma dokokin kasa da kasa da aka amince da su.