Iran Ta Yi Allah Wadai Da Laifukan Isra’ila A Kasar Lebanon

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah wadai da laifukan da ‘yan sahayoniyya suka aikata a Lebanon Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah wadai da laifukan da ‘yan sahayoniyya suka aikata a Lebanon

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da ci gaba da kai hare-haren soji da ‘yan Sahayoniyya suke kai wa Lebanon, gami da munanan hare-haren da aka kai a ‘yan kwanakin nan kan yankunan zama a kudancin kasar, wanda ya yi sanadiyyar shahada da kuma raunata ‘yan kasar Lebanon da dama, ciki har da mata da yara.

Bayanin Ma’aikatar Harkokin Wajen ya jaddada cewa: “Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da ci gaba da kai hare-haren soji da ‘yan Sahayoniyya suke y ikan Lebanon, musamman hare-haren ta’addanci da aka kai a ‘yan kwanakin nan kan unguwanni da wuraren zama a kudancin Lebanon, wadanda suka janyo shahada tare da raunata fararen hula da dama, ciki har da mata da yara. Yayin da take yabawa ‘yan gwagwarmaya da juriyar al’ummar Lebanon kan yanayin juriyar mulkin kama-karya na yahudawan sahayoniyyar Isra’ila da ke kashe yara, Ma’aikatar ta sake jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga Lebanon wajen kare ikonta na kasa, hadin kai, da kuma cikakken ‘yancin yankinta.”

Bayanin ya ci gaba da cewa: “Hare-haren ta’addanci da ‘yan Sahayoniyya suka kaddamar kan Lebanon da kuma mamaye wasu sassan wannan kasar, tare da aikata manyan laifukan yaki, an aiwatar da su ne da goyon bayan Amurka.” Saboda haka, gwamnatin Amurka babbar abokiyar hulɗa ce a cikin laifukan da ‘yan Sahayoniyya suka aikata a Lebanon, kuma dole ne a ɗora mata alhakin wannan rawar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted