Iran ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa ‘yan jarida a Gaza

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa ‘yan jarida  biyar a wani harin da Haramtacciyar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa ‘yan jarida  biyar a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai a zirin Gaza, yana mai bayyana wannan laifi a matsayin shaida ta yanke kauna daga  gwamnatin da duniya ta juya mata baya saboda munanan laifukanta.

A wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta a yammacin wannan Litinin, Araghchi ya bayyana cewa kisan gillar da aka yi wa wasu manyan ‘yan jarida na Falasdinu ba alama ce ta karfin gwamnatin sahyuniya ba, hakan alama ce ta gazawa da yanke kauna.

Ya kuma kara jaddada cewa hadin kan da wasu gwamnatocin kasashen Yamma suke baiwa Isra’ila yana mai ishara da kasashe irin su Amurka, da cewa hakan shi ne  ke kara karfafa gwiwar Haramtacciyar Kasar Isra’ila wajen ci gaba da tafka laifuka yakin kisan kare dangi a kan al’ummar Falastinu.

Su ma a nasu bangaren Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin yahudawan ta dauka na kaddamar da yaki a kan ‘yan jarida, tare da yin tir da kasashen da suke ikirarin kare hakkokin bil adama da fadar albarkacn baki.

Rundunar IRGC ta bukaci kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama da su tofa albarkacin bakinsu tare da daukar matakin dakatar da laifukan yaki na gwamnatin sahyuniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted