Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Nasir Kan’ani ya yi tir da kakkausar murya akan harin ta’addancin da HKi ta kai wa unguwar “Dhaniya” dake birnin Beirut da marecen jiya juma’a.
Kan’ani ya kara da cewa; Harin dabbanci wanda fandararrun ‘yan sahayoniya su ka kai ta hanyar amfani da bama-baman da Amurka ta ba su, yana cin karo da dokokin kasa da kasa,sannan kuma keta hurumin kasa ce mai cin gashin kanta.”
Har ila yau, Kan’ani ya kara da cewa; Babu shakka Amurka tana tare da ‘yan sahayoniya a laifukan da suke aikatawa, don haka ya zama wajibi a hukunta su.”
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Yadda ‘yan sahayoniyar suke cigaba da aikata laifuka a Falasdinu da Lebanon yana nuni da cewa kiraye-krayen da Amurka take yi na a tsagaita wutar yaki, ba komai ba ne sai yaudara domin bai wa HKI lokaci ta cigaba da aikata abinda take yi.”
Bugu da kari kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce; rashin dauka mataki akan HKI ne ya ba ta damar cigaba da laifukan da take yi a Falasdinu da kuma Lebanon.