Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi Allah wadai da laifukan da kungiyar ‘yan Sahayoniyya ke aikatawa kan Falasdinawa
Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa tana yin Allah wadai da laifukan da kungiyar ‘yan Sahayoniyya ke aikatawa kan al’ummar Falasdinawa.
Sanarwar ta ce: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana yin tofin Allah tsine da tsananin Allah wadai da kuma bayyana damuwa game da ci gaba da laifukan kungiyar ‘yan Sahayoniyya ke aikatawa kan al’ummar Falasdinawa tare da yin Allah wadai da ayyukan kisan kare dangi, laifukan yaki, da laifukan cin zarafin bil’adama a yankin Gaza da Yammacin Kogin Jordan.”
Ma’aikatar ta kuma yi Allah wadai da harin da kungiyar ‘yan Sahayoniyya ta kai kwanan nan kan Masallacin Al-Aqsa da kuma lalata wannan wuri na Masallacin mai tsarki.
Sanarwar ta nuna ci gaba da goyon bayan sojoji, kudi, da siyasa da wasu kasashe ke bayarwa ga kungiyar ‘yan Sahayoniyya a matsayin manyan laifuffuka, tana mai jaddada cewa al’ummar duniya tana da alhakin daukar mataki don dakatar da wadannan ayyuka da kuma tallafawa hakkokin al’ummar Falasdinawa. Ma’aikatar ta yi kira da a sanya takunkumi da kuma daukar alhakin wadanda suka aikata laifuka kan Falasdinawa, tana mai jaddada cewa kare hakkin bil’adama da magance keta dokokin