Kotu a Iran ta bukaci Amurka da ta biya sama da dala biliyan 290, a matsayin diyya ta hare haren da kawacen Amurka da Isra’ila suka kai kan kasar.
An bayyana hakan ne a wani bikin rantsar da lauyoyi 505 da aka gudanar a Tehran, inda Hassan Abdolian-Pour, darektan kungiyar Lauyoyi, Masana da Masu Ba da Shawara Kan Iyali ta Kotun Shari’ar Iran, ya bayyana matakan da cibiyar ta dauka don fara shari’ar laifukan da sojojin Amurka da gwamnatin Isra’ila suka aikata kan Iran, a kotunan kasa da kasa.
Makiya sun kai hari ga cibiyoyin kimiyya da dama, ciki har da Jami’ar Sharif, Jami’ar Kimiyya da Fasaha, da Jami’ar Masana’antu da Ma’adanai, kuma mun binciki duk waɗannan wuraren.” Inji shi
Mista Abdolian-Pour ya kuma ambaci Tofigh Darou, wani kamfanin magunguna, a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da aka tantance.
Ya yi tambaya dalilin da ya sa aka kai hari ga wannan kamfanin, yana mai cewa yana ƙera magunguna na musamman ga marasa lafiya da ke fama da cututtuka masu tsanani.
Ya nuna cewa Iran tana bin diddigin shari’a ba kawai a kotunan ƙasa da ƙasa ba, har ma a ƙarƙashin dokar Iran, wanda, a cewarsa, yana ba kotunan ƙasa damar bincika shari’o’in da suka shafi laifukan Amurka.