Iran Ta Turkiyya Sun Tattauna Kan Batun Syria

Kasashen Iran da Turkiyya, sun tattauna kan batun kasar Siriya tun bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Assad. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi a wata

Kasashen Iran da Turkiyya, sun tattauna kan batun kasar Siriya tun bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Assad.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi a wata zantawa da takwaransa na Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada wajabcin kare hakkin gungun tsiraru a Syria karkashin sabuwar gwamnatin kasar.

A yayin tattaunawar, manyan jami’an diflomasiyyar biyu sun tattauna kan dangantakarsu da kuma sabbin abubuwan da suka faru a kasar Siriya.

Ministan harkokin wajen na Iran Ya kuma yi kira da a kawo karshen rigingimun da ke faruwa a tsakanin kungiyoyi daban-daban a Syria.

Araghchi ya bayyana bukatar kafa gwamnatin Syria da za ta hada da dukkanin kungiyoyin siyasa, kabilanci da addinai.

Araghchi ya kuma nuna damuwarsa kan rahotannin da ake samu game da matakan da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai suka dauka kan fararen hula a yankunan Siriya da ke karkashin ‘yan Shi’a da Alawiyyawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments