Iran Ta Taya Kungiyar Hamas Murnar Samun Nasara A Kan HKI A Yakin Watanni Kimani 16

Ministan harkokin wajen Kasar Iran ya tana kungiyar Hamasa murnar samun nasara a kan HKI bayan yakin watanni kimnai 15 da kuma shahadar fiye da

Ministan harkokin wajen Kasar Iran ya tana kungiyar Hamasa murnar samun nasara a kan HKI bayan yakin watanni kimnai 15 da kuma shahadar fiye da Falasdinawa 46,000, ko kuma kissan kare dangi.

Abbas Argchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana haka ne a zantawa ta wayar tarho da yayi da Khalid Al-Hayya mataimakin shugaban kungiyar kwana guda bayan an shalanta tsagaita wuta a yakin na Gaza.

Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana yabawa Falasdinawa a Gazamgaba dayansu wadanda suke dauke da makami da kuma fararen hulan mata da yara wadanda cikinsu ne aka fi samun shahidai.

A nashi bangaren Khalali Al-Hayya ya godewa JMI da kasancewa tare da Falasdinawa tun farkin yakin ahr zuwa karshensa. Ya kuma yabawa sauran kungiyoyin masu gwagwarmaya da suka tallafamata a wannan yakin, wadanda suka hada da, Yemen Iraki da kuma Hizbullah.

A ranar laraban da ta gabata ce Firaiministan kasar Qatar wanda da shi da jami’an gwamnatin kasar Masar suka yi fadi tashi don shiga tsakani da kuma tabbatar da tsagaita wutan, wanda yake da marhaloli 3 kuma za’a dauki kwanaki 42 ana aiwatar da shi. A ciki banda tsagaita wuta za’a yimusayar fursinoni, 1000 a gaza, da kuma wasu daruruwan da ake tsare da su tun lokaci mai tsawo.

Gwamnatin Kasar Yemen Ta Yabawa Falasdinawa Masu Gwagwarmaya A Gaza, Ta Kuma Ja Kunnen HKI.

Gwamnatin kasar Yemen ta yabawa mayaka Falasdinawa daga kungiyoyi daban daban da kuma sauran falasdinawa mata da yara wadanda suka jurewa yaki da HKI na tsawon watanni 15.

Gwamnatin ta kara da cewa, tsagaita wuta wacce aka samar bayan watani 15, babban nasara ce ga Falasdinawa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa dubban mutanen a birnin Tehran na kasar Iran ne, suka fito kan tituna a kuma dandalin falasdinu a nan tsakiyar Tehran a jiya Alhamis, inda suka taru don taya Falasdinawa murnar samun yarjeniyar tsagaita wutar da HKI, bayan yaki na kwanaki 465.

A yau Jumma’a ma, ana saran miliyoyin mutanen kasar zasu fito kan tituna bayan sallar Jumma’a don nuna goyon  bayansu ga Falasdinawa a Gaza, da kuma tayasu murnar tsagaita wuta da HKI..

Sai dai wasu labarai sun bayyana cewa jiragen yakin HKI sun ci gaba da kai hare-hare kan mutanen gaza duk tare da sanarwan tsagaita wuta,  da aka yi a Gaza. Inda falasdinawa kimani 46000 suka yi shahada. Sannan wasu kimani 100 000 suka ji rauni.  A ranar lahadi mai zuwa ne za’a fara aiwatar da tsagaita wutar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments