Iran Ta Soki Shirun Turai Kan Kokarin Amurka Na Rusa Kotun ICC

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rashin daukar mataki na Turai wajen hana hukunta kotun hukunta manyan laifuka ta Hague ya gwada tana da

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rashin daukar mataki na Turai wajen hana hukunta kotun hukunta manyan laifuka ta Hague ya gwada tana da hannu wajen karya doka da adalci

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rashin daukar mataki na Turai game da takunkumin da aka sanya wa Kotun hukunta manyan laifuka ta Hague ya gwada tana da hannu wajen karya doka da adalci. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi tsokaci kan sabbin takunkumin da Amurka ta kakaba wa Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da kuma barazanar wargaza ta.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Mehr, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi tsokaci kan sabbin takunkumin da Amurka ta kakaba wa Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da kuma barazanar wargaza ta, yana mai cewa: “Marco Rubio ya yi barazanar cewa idan kawayen Amurka ba su dage kan ICC ba, to Amurka za ta wargaza ta.

Abin lura shi ne, idan aka tuna shekarun 1930: tsarin kasa da kasa ya ruguje ba wai kawai sakamakon zalunci ba ne, har ma lokacin da aka mayar da yin amfani da karfi ya zama al’adan yau da kullum, duniya kuma ta yi shiru kan hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted