Iran ta soki matakin Amurka na hana ta shigar da wutar lantarki Iraki

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta dauka na janye sassaucin da ta yi wa Iraki na shigo

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta dauka na janye sassaucin da ta yi wa Iraki na shigo da wutar lantarki daga Iran.

Araghchi ya bayyana matakin da gwamnatin Trump ta dauka a matsayin “abin takaici.”

Ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta na kokarin hana al’ummar iraki samun ababen more rayuwa kamar wutar lantarki, musamman gabanin watanni masu zafi na wannan shekara.”

Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Iraki.

Ya kara da cewa Iran ta tsaya tsayin daka kan kudurin ta ga gwamnatin Iraki na dakile ayyukan Amurka da suka sabawa doka.

Kalaman Araghchi sun zo ne bayan da Amurka ta sanar da janye sassaucin da ta yi wa Iran wanda ya bai wa Iraki damar shigo da wutar lantarki daga makociyarta ta gabas.

A martaninsa, shugaban kwamitin kudi na majalisar dokokin Iraki ya yi gargadin cewa duk wani mataki da Washington za ta dauka na takaita shigo da wutar lantarki daga Iran zai haifar da rugujewar wutar lantarki a Iraki.

A halin yanzu, kusan kashi 80 cikin 100 na makamashin da ake samu a Iraki ya dogara ne da iskar gas, wanda hakan ya sa kasar ta dogara sosai da Iran don ci gaba da samar da wutar lantarki.

A watan Yulin 2022, Iraki ta sanya hannu kan kwangilar shekaru biyar da Iran don samar da megawatt 400 na wutar lantarki.

A watan Maris din shekarar 2024, an cimma wata yarjejeniya ta kara yawan iskar gas din Iran zuwa mita cubic miliyan 50 a kowace rana, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 6 a duk shekara.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments