Iran Ta Shirya Harba Taurarin Yan’adam Guda Uku Zuwa Sararin Samania A Lokaci Guda

Iran ta shirya tsab don cilla taurarin yan’adam guda uku a lokaci guda zuwa sararin samania a cikin mako mai zuwa 28 ga watan Decemban

Iran ta shirya tsab don cilla taurarin yan’adam guda uku a lokaci guda zuwa sararin samania a cikin mako mai zuwa 28 ga watan Decemban da muke ciki.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ne ya bada wannan rahoton a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa taurarin yan’adam Tolou-3, Zafar-2 da kuma Kawthar 1.5 zasu tashi zuwa sararin samania ne da misalign karfe 4.48 na yamma a nan Tehran, wato karfe 1.18  agogon GMT a ranar Lahadi 28 ga watan Decemba da muke ciki. Kuma za’a yi amfani da kumbo ko Rocket mai suna ‘Soyuz’ a gabacin kasar Rasha.

Labarin ya kara da cewa tauraron Tolou-3 shi ne tauraro mafi nauyin wanda Iran zata aika zuwa sararin samaniyya kuma yana da nauyin kilogram 150. Tauraron wanda na daukar hotunan doron kasa ne yaka da karfin ido na hangen nesa har na mita 5 a hotunan baki da fara, sannan mita 10 ga hotuna masu launuka.

Labarin yace hotunan da zai dauka zai yi amfani a ayyukan noma da kuma kula da gonaki, gano ruwa da kuma tsiminsa, haka ma zai kula da aukuwan musibun sama kamar guguwar iska da kuma ambaliyan ruwa.

Sai kuma Zafar-2 wanda aka samar da shi a jami’ar kimiya ta Iran shi ne daukar hotunan doron kasa ne inda zai iya gano inda ma’adinai suke da kuma nau’o’insu.  Sai kuma Kauthar wanda yake yada internet ta IoT.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted