Gwamnatin kasar Iran ta kai korafi a gaban hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da yakin da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar na tsawon kwanaki 12, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da 600.
Nasir Siraj wani jami’in ofishin jakadancin Iran a MDD ya mikawa kwamitionan hukumar Volker Türk a jiya Jumma’a .
Kafin haka dai ministan kiwon lafiya na kasar Iran ya bayyana cewa mutane 627 suka rasa rayukansu a yayinda wasu 4,870 suka ji rauni a yakin kwanaki 12 wanda wadannan kasashe biyu suka keta hurumin sararin samaniyar kasar. Yakin ya zo karshe ne bayan da HKI ta shelanta tsaida yaki ita kadai.
Korafin ya bayyan cewa abinda wadannan kasashe biyu suka yi ya sabawa dokokin kasa da kasa da dama, daga ciki har da dokar kasa da kasa ta kare hakkin bil’adama.