An Fara Gudanar Da Jana’izar Shahidan Yakin Kwanaki 12 A nan Tehran

A safiyar yau ne aka gudanar da tattakin jana’izar shahidai kimani 60 a nan Tehran, wadanda suka hada da kwamandojin sojojin kasar da da masana fasahar Nukliya da sauran mutane maza da mata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto cewa, an fara tattakin Jana’izar ne daga danganlin inkilabi ko juyin juya hali […]

Iran ta Ki Amincewa Da Ziyarar Shugaban Hukumar IAEA Zuwa Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, yana daukar shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA Rafael Grosi a matsayin wanda ya ingiza HKI kaiwa kasar Iran hare-hare a ranar 13 ga watan Yuni. Ya kuma kara da cewa, Grossi a halin yanzu ya matsa yana son zuwa kasar Iran don ya […]

Iran Ta Shigar Da Korafi A Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta MDD

Gwamnatin kasar Iran ta kai korafi a gaban hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da yakin da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar na tsawon kwanaki 12, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da 600. Nasir Siraj wani jami’in ofishin jakadancin Iran a MDD ya mikawa kwamitionan hukumar Volker Türk  a jiya […]

An Bude Juyayin Ashura A Fadin Iran

A ranar farko ta watan Muharram, an bude juyayin Ashura ta hanyar yin taron kananan yara a matsayin nuna  juyayi ga jaririn Imam Hussain          ( a.s)  Ali Asgar ( a.s) da abokan gaba su ka kashe a Karbala. Iyaye mata dauke da kananan yaransu  masu watanni  6 daga  haihuwa sun cika wurare mabanbanta na Iran […]

Limamin Tehran:  Duniya Ce Ta Yi Yaki Da Iran

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya bayyana cewa; A cikin kwanaki 12 da su ka gabata duniya ce ta yi yaki da Iran. Hujjatul Islam Wal Muslimin   Abu Turabi Fard, ya fara hudubarsa da mika sakon ta’aziyyar shigowar ranakun Ashura, haka nan kuma jinjina ga shahidan jamhuriyar musulunci masu daraja da HKI ta […]

 Kananan Yara 2 Falasdinawa  Masu Shan Nono Sun Yi Shahada Saboda Yunwa

Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada. Majiyar asibitin Nasar ta a  birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina […]

 Arakci:  Idan Aka Kai Iran Bango Za Ta Fito Da Hakikanin Karfin Da Take Da Shi

Minsitan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kira yi shugaban kasar Amurka Donald Ttump da ya daina yin maganganun da ba su dace ba akan jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei. Abbas Arakci ya kara da cewa; Ko kadan  Tehran ba za ta bari wani mahaluki ya ayyana mata makoma ba, […]