Iran Ta Shigar Da Kara Kan Tabbatar Da Kisan Isma’ila Haniyya Wanda HKI Ta Yi

Jakadan JMI a MDD Amir Sa’ed Iranvani ya rubuta wasika ga babban sakataren MDD Antonio Gutteree da kuma shugaban kwamitin tsaro na kwamitin tsaro na

Jakadan JMI a MDD Amir Sa’ed Iranvani ya rubuta wasika ga babban sakataren MDD Antonio Gutteree da kuma shugaban kwamitin tsaro na kwamitin tsaro na MDD a wannan watan,  inda ya gabatar da korafin Tehan dangane da tabbatarwan da HKI ta yi a ranar litinin da ta gabata kan cewa itace ta kashe shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya wanda ya ziyarce kasar Iran don halattan taron bukin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pazeskiya na a birnin Tehran.

Kafin haka dai HKI ta yi gum da bakinta, kan kissan. Amma a ranar litnin data gabata 23-12-2024 ministan tsaron HKI Yisrael Katz ya tabbatarwa duniya kan cewa gwamnatinsa ce ta kashe Isma’ila Haniyya da Yahya Sinwar shuwagabannin kungiyar Hamas da kuma Sayyid Hassan  Narallah shugaban Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da Sayyid Safiyyudaeen shugaban majalisr zartarwa ta kungiyar Hizbullah da sauran kwamadojin kungiyoyin biyu sannan ya kara da cewa haka zasu yi da da shuwagannin kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen.

A cikinm wasikar Irawani ya shaidawa babban sakataren da kuma kwamitin tsaro kan cewa. Iran tayi dai-dai a lokacinda ta maida martani da hare-haren wa’adu sadik na 2. Tare da dogaro da kuduri mai lamba 51 na MDD, wanda ya bawa ko wace kasa damar kare kanta kan wanda ya tsokaneta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments