Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Kan Jiragen Makiya

babban kwamandan kasar iran yace dakarun sojin kasar za su ci gaba da mayar da martani kan jiragen ruwan makiya

Babban kwamandan soji na kasar Iran real admiral habibollah sayyari ya bayyana cewa kasar iran ta kai harin kan jiragen ruwan makiya a mashigar hurzmu kuma za ta sake kai musu hari idan aka ci gaba da daukar matakai a kanta,domin kare kasarta

Ya ce dakarun sojin kasar iran suna cikin shirin daukar mummunan matakai kan jiragen ruwan makiya,  kuma yayi gargadin cewa idan wani abu ya kara samun kasar iran a nan gaba to ba za ta yi kasa aguiwa ba wajen mayar da martani nan take,

Haka zalika sayyari ya jaddada cewa duk lokacin da bukata ta taso zamu dauki matakin kai hare hare kan makiya, har yanzu dakarun tsaron kasar iran suna ci gaba da kula da mashigar hurmzu tun daga lokacin Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare hare kan iran a watan fabareru.

Daga karshe dakarun kare juyin musulunci na Iran sun yi  gargadi cewa wuta na jiran duk wata tankar mai da ta yi kokarin keta kaidoji da tsaron da aka shinfida a mashigar ta Hurmuz

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted