Iran Ta Sami Nasarar A Kan Amurka A Gasar Volleyball Na Kasa Da Kasa

Kungiyar wasan Volleyball na kasar Iran sun sami nasarar kaiwa da wajen karshe a gasar FIVB ta duniya bayan ta lallasa kungiyar kwallon Vallibal ta

Kungiyar wasan Volleyball na kasar Iran sun sami nasarar kaiwa da wajen karshe a gasar FIVB ta duniya bayan ta lallasa kungiyar kwallon Vallibal ta kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an tashi gasar da Iran 3 Amurka 0.

Labaran ya kara da cewa Iran ta sami nasarar mamayar wasan kusa da na Karshe a gasar gaba daya. Sakamakon ya nuna cewa kungiyar kwallon Vollyball na kasar Iran ta sami horaswa mai kyau a wannan fagen har ta kai marhalar wasannin kasa da kasa.

Za’a gudanar da gasar karshe tsakanin Iran da Italia a dai dai lokacinda kungiyoyin biyu suna da maki iri daya.

Iran a cikin yan shekaru da suka gabata ta tashi a nahiyar Asia a matsayin kungiyar Vollyballa mai karfi. Sannan ta shiga fagen kasa da kasa a halin yanzu. Tare da fatan watarana tana iya daukar kufin gasar ta FIVB .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments