Kakakin cibiyar sojan Iran ta Khatamul-Anbiya, ya sanar da cewa; Mashigar ruwan Hurmuz ta koma yadda take a karkashin tsaro mai tsanani.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; Dama Iran ta bude mashigar ruwan ne da zummar nuna kyakkyawan fata, domin barin wani adadi kadan na jiragen ruwa na jigilar man fetur da na kasuwanci ya wuce, sai dai abin takaici Amurka ta sake komawa kan halayyarta ta fashi da makami a doron ruwa, da sunan killace tasoshin jiragen ruwan Iran.
Kakakin cibiyar sojan ya kuma ce; Matukar Amurka ba ta bari jiragen ruwa da suke zuwa da kuma fita tasoshin jiragen ruwan Iran ba, to mashigar ruwan za ta ci gaba da zama a rufe.