Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun kaddamar da wasu sabbin hare-hare na makamai masu linzami a kan gwamnatin yahudawan sahyoniya a cikin daren jiya Lahadi.
An jiyo karar fashewar abubuwa masu karfi a yankunan da aka mamaye na Upper da Lower Galilee, Haifa, Afula da Nazaret.
Jim kadan bayan hare-haren, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun kaddamar da wasu sabbin hare-haren jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami kan Tel Aviv, Haifa da wasu yankuna da dama a kudancin yankunan da aka mamaye.
Harin dai na daga cikin matakai da dama na harin ramuwar gayya da Iran ta kaddamar tun ranar Juma’a a matsayin martani ga harin Isra’ila wanda ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran, sansanonin soji dama wuraren zama a Tehran babban birnin kasar dama wasu sassa.
Harin ramuwar gayya na Iran ya fara ne jim kadan bayan jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a gidan talbijin, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatin Isra’ila zata fuskanci martini bisa babban kuskuren data aikata na shelanta yaki kan Iran.