Search
Close this search box.

Iran Ta Nanata Kudirinta Na Goyan Bayan Kungiyoyin Gwagwarmaya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya nanata kudurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya. Araghchi ya bayyana haka ne a

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya nanata kudurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya.

Araghchi ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da Sayyed Abdallah Safieddine, wakilin kungiyar Hizbullah a Iran a jiya Lahadi.

Safieddine ya mika sakon taya murna daga babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah zuwa Araghchi bisa nadin da aka yi masa a matsayin ministan harkokin wajen kasar, inda ya yi masa fatan samun nasara a wannan sabon mukamin nasa.

A nasa martanin, Araghchi ya bayyana jin dadinsa da fatan alheri tare da mika gaisuwar sa ga Sayyed Nasrallah da mayakan gwagwarmayar Lebanon.

Ya kuma kara jaddada goyon bayan Iran ga kungiyar Hizbullah da sauran kungiyoyin a gwagwarmayar da suke yi da wuce gona da iri da Isra’ila ke yi.

Tattaunawar da aka yi tsakanin Araghchi da Safieddine ta mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a yankin musammam a baya-bayan nan, tare da mai da hankali sosai kan hare-haren Isra’ila a Lebanon, da kisan kiyashin da take ci gaba da yi a Gaza, da kuma halin da ake ciki a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments