Iran Ta Musanta Rahotannin Ganawar Elon Musk Da Kakadan Kasar A MDD

Iran ta musanta rahotannin dake cewa an yi wata ganawa tsakanin Elon Musk da jakadan kasar a MDD. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghaei

Iran ta musanta rahotannin dake cewa an yi wata ganawa tsakanin Elon Musk da jakadan kasar a MDD.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghaei shi ne ya yi watsi da rahotannin da kafafen yada labarai na yammacin duniya suka fitar kan ganawar da aka bayyana da ta sirri tsakanin Elon Musk da jakadan Iran din a MDD.

A wata hira da ya yi da kamfanin dilancin labaren kasar na IRNA, Baghaei ya bayyana mamakinsa kan yadda kafafen yada labaran Amurka ke yadawa kan ganawar da ya musanta yana mai cewa karya ce.

A ranar Juma’a, ne kafofin yada labaran yammacin duniya suka nakalto jaridar New York Times tana mai cewa, Elon Musk, shugaban sashen rage kashe kudade na Donald Trump da aka kafa ya gana da jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir-Saeed Iravani a wani wuri na sirri a birnin New York.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments