Iran Ta Mayar Da Martani Akan Zarginta Dangane Da Yemen

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi ma ta dangane da kasar Yemen.  A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi ma ta dangane da kasar Yemen.

 A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta fitar ta bayyana cewa: Abinda mutanen Yemen suke yi domin taimakawa al’ummar Falasdinu, mataki ne na kashin kansu da su ka dauka cikin ‘yanci saboda lamirinsu na ‘yan adamtaka da kuma taimako na musulunci ga ‘yan’uwansu Falasdinawa.”

Bayanin ya kuma ci gaba da cewa; Jinginawa jamhuriyar musulunci ta Iran abinda mutanen na Yemen suke yi, ba shi da tushe, kuma manufar hakan ita ce, rufe laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi a Falasdinu.”

Bayanin ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci tana sake jaddada matsayarta akan wajabcin kiyaye da karrama kasashe da kasantuwarsu a dunkule a wuri daya, kamar kuma yadda muke yin tir da hare-haren sojan Amurka akan Yemen, domin hakan take dokokin MDD ne, da kuma dokokin kasa da kasa.”

Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta yi kira da a kawo karshen kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa da shi ne tuhsen rashin zaman lafiya a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.

Wani sashe na bayanin na ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran din ya ce; al’ummar Iran a shirye suke, su kare kansu daga duk wata barazana akan manufofin kasa, kuma alhakin duk abinda zai faru yana wuyan hukumomin ‘yan ta’adda na Amurka da sahayoniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments