Iran, Ta La’anci Harin Da ‘Yan Ta’adda Suka Kai Karamin Ofishin Jakadancinta A Aleppo

Iran, ta yi tir da harin da ‘yan ta’adda suka kai a karamin ofishin jakadancinta na birnin Aleppo a kasar Siriya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen

Iran, ta yi tir da harin da ‘yan ta’adda suka kai a karamin ofishin jakadancinta na birnin Aleppo a kasar Siriya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baqai, ya yi kakkausar suka kan harin.

Ya bayyana harin a matsayin wanda “ba za a amince da shi ba” tare da bayyana shi a matsayin keta yarjejeniyar Vienna kan huldar jakadanci (1963), wanda ya haramta irin wadannan hare-hare kan wuraren diflomasiyya da wakilai.

Da yake amsa tambaya dangane da yanayin lafiyar ma’aikatan karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Aleppo, jami’in diflomasiyyar ya ce: karamin jakadan da dukkanin membobin karamin ofishin jakadancin da ke birnin Aleppo suna cikin koshin lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments