Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragchi ya rubutawa babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC Hussain Ibrahim Taha, da kuma tokwarorinsa na kasashen Saudiya da Turkiya, Faisal bin Farhan da kuma Hakan Fidan wasiku dangane da bukatar kasashen kungiyar su gudanar da taron gaggawa kan abinda ke faruwa a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa, saboda yadda HKI take kara takurawa mutanen Gaza, tana kara daukan matakan keshesu, mung a akwai bukatar kasashen musulmi sun dauki matakai fiye da na baka, wato fadar ‘All..wadai ” kadai. Yakamata kasashen musulmi su dauki matki fiya da haka wanda za’a ganshi a aikace kan Falasdinawa na gaza.
Su dauki mataki wanda zai kai ga dakatar da yaki a gaza da kuma kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa.
Yace abinda yake faruwa a Gaza a halin yanzun sun hada da hare-hare ta sama da ci gaba da toshe hanyoyin shigo da abinci gaza wanda ya kai ga falasdinawa suna mutuwa saboda yunwa.
Yace yawan mutanen da sojojin yahudawan suke kashewa ya na kara yawa a ko wace rana, wanda adadin wadanda suke kashewa a kisa da makami a wajen karban abincin agaji yana karuwa a duk wat araba.
Ya ce wannan halin yana bukatar daukar mataki daga kasashen musulmi.wanda zai kawo karshen wanan abin, kuma akwai labarin da ke cewa HKI tana son kwace gaza kwata-kwata daga hannin Hamas. Ta maida shi kamar yankin yamma da kogin jodan.