Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi jakadun kasarta a kasashen Biritaniya, faransa da kuma jamus domin tuntuba, a daidai lokacin da takun tsaka tsakaninta da kasashen ke kara kamari sanadin yunkuinsu na ganin an sake dawo ma Iran da takunkuman MDD.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar yau Asabar ta ce “Bayan matakin rashin da’a da wasu kasashen Turan uku suka dauka na cin zarafin yarjeejniyar nukiliyar 2025 na JCPOA na maido da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka soke, an gayyaci jakadun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Jamus, Faransa da Birtaniya zuwa Tehran.”
A ranar Juma’a, Amurka, Birtaniya, Faransa, Denmark, Girka, Panama, Saliyo, Slovenia, da Somaliya sun yi watsi da daftarin matakin da Rasha da China suka gabatar wanda ke neman jinkirta aiwatar da matakin kan Iran na tsawon watanni shida.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, (yanzu) matakin zai fara aiki, wanda zai sake sanya takunkumi kan Tehran a karshen wannan makon nan, bayan kawo karshen shirin hadin gwiwa na Action (JCPOA).”