Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta kira jakadan Burtaniya a Tehran inda ta isar masa da sakon korafi kan jawaban firay ministan kasar dangane da JMI. Iran ta yi tir da zancen firay ministan kasar Burtania, kuma ta kira Hugo Shorter jakadan Burtaniya a Tehran don hakan.
Majid Takhtravanci mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren harkokin siyasa ne ya zauna da shorter ya kuma isar da wannan sakon ga gwamnatin kasar Burtaniya.
Ravanchi ya bayyana cewa, kokarin dulmuya JMI cikin abubuwan da suka faru a sansanin jiragen yakin na ‘Fairford’ ba zai kauda batun fallasa hannun gwamnatin kasar wajen kashe Iraniyawa a yakin da ya gabata wanda Amurka da HKI suka jagoranta.
Yace Iraniyawa suna da hakkin neman gwamnatin kasar Burtania ta amsa tambayoyi kan kissan su da kuma irin rawan da ta taka wajen wannan kissan. Ma’aikatar ta bukaci gwamnatin kasar Burtania ta bayyana dalilan da suka sa take tsanin adawa da JMI a baya bayan nan da kuma kafin haka.
Kafin haka dai Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya musanta cewa, Iran tana da hannu a cikin abinda ya faru a sansanin sojoji na RAF Fairford. An kama mutane 5 dangane da lamarin gaba dayansu matasa yan shekaru 23-25 anna an bada bekinsu.