Iran Ta Kera Jiragen Sama Marasa Matuka Ciki Masu Tashi Da Sauka A Teku

Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Jiragen saman yaki marasa matuka ciki na Iran zasu iya tashi da sauka a teku Ministan tsaron kasar

Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Jiragen saman yaki marasa matuka ciki na Iran zasu iya tashi da sauka a teku

Ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samar da jiragen saman yaki marasa matuka ciki da ake amfani da su wajen aikin tsaro da ya wasu ayyuka na daban, kuma jirage ne da suke da karfin tashi da sauka a teku.

A yayin bikin mallakawa rundunar sojin Iran jiragen sama marasa matuka ciki guda 1,000, Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya taya ministan tsaron Iran murnar zagayowar ranar haihuwar shugaban Muminai Imam Ali dan Abi-Talib (a.s) inda ya ce: An samu ingantaccen kuma cikakken hadin kai da taimakekkeniya tsakanin masana’antar tsaro da rundunar sojojin Iran, kuma an mallakawa rundunar sojin jiragen saman yaki marasa matuka ciki guda 1,000 don bunkasa dabarun yaki sakamakon wannan gagarumin hadin kan.

Janar Aziz ya kara da cewa: Sojojin Iran sun kai wani mataki na ci gaba wajen amfani da jiragen sama marasa matuka ciki, inda suke sarrafa jiragen yaki iri-iri masu dauke da dabaru daban-daban masu alaka da kere-kere na musamman ga dakarunsu na kasa da sama da kuma na ruwa domin tsaron kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments