Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana cewa; Babu yadda za a fitar da sanadiyar Uranium na Iran zuwa wajen kasar.
A wata hira da tashar talabijin ta kasar Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran din ya ce’ ko kadan babu gaskiya a cikin batutuwan da suke fitowa daga bakunan wasu jami’an gwamnatin Amurka na cewa za a fitar da sanadarin urani’um daga kasar Iran’ sannan ya kara da cewa; Babu yadda za a yi mu amince da fitar da tataccen sanadarin uranium zuwa waje ta kowane yanayi, kuma kamar yadda kasa ta Iran take da tsarki a wurinmu, haka nan wannan batun yake da muhimmanci a wurinmu.”
Dr.Baka’i ya ce; ko kadan ba mu bijiro da batun mika tataccen sanadarin uranium ga Amurka ba,amma da akwai wasu shawarwari masu yawa da aka bijiro da mu akan batun.