Iran Ta Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Samfurin MQ-1 A Kudancin Kasar

Dakarun karare sararin samaniyar JMI sun bada labarin kakkabo jirgin yakin Amurka samfurin MQ1 a sararin samaniyar lardin Hurmuzghan a yau da safe. Kamfanin dillancin

Dakarun karare sararin samaniyar JMI sun bada labarin kakkabo jirgin yakin Amurka samfurin MQ1 a sararin samaniyar lardin Hurmuzghan a yau da safe.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto dakarun na cewa, wannan jirgin yana da matukar muhimmanci ga Amurkawa, saboda irin aikin da suka yi da shi a kasar Afganistan na kashe mutane da lalata wurare.

Kuma yana iya zuwa tazarar kilomita 20,000 a lokacin yana iya zagaya ko ina a kasar Afganistan ya kuma kashe wanda ya yaga dama.

Mutanen Afganistan a lokacin suka kiransa mahaucin Kandahar.

Masana suna ganin bayan da dakarun kare sararin samaniyar kasar Iran sun kakkabo samfurin MQ 9 da dama, a  cikin wannan yakin wannan ya sa suka maye shi da MQ 1. Sai dai abin sani a nan shi ne, a wajen dakarun kare sararin samaniyar JMI kakkabosu duk daya ne a wajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted