Iran Ta Kakkabo Jiragen Yakin HKI Fiye Da 196 A Yakin Kwanaki 12

Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta kakkabo jiragen yakin HKI fiye da 196 a cikin yakin kwanaki 12 da aka dora mata a

Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta kakkabo jiragen yakin HKI fiye da 196 a cikin yakin kwanaki 12 da aka dora mata a cikin watan Yunin da ya gabata. Daga ciki har da jiragen yaki samfurin Heron da Hermes -900 wadanda ke aiki da kayakin zamani.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wata tashar talabijin ta cikin gida tana fadar haka a yau Asabar ta kuma kara da cewa

Sashen garkuwar sararin samaniya na sojojin sama sun nuna hutunan lokacin da suke kakkabo jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na HKI a lokacinda suka shigo sararin samaniyar kasar kafin su kai ga bararsu.

Burgediya Janar Reza Khajeh mataimakin kwamandan garkuwar sararin samaniya na sojojin kasar Iran yace sun kakkabu fiye da jiragen yaki 196 a cikin yakin.

Khajeh ya kara da cewa nan gaba kadan zamu kaddamar da garkuwan sararin samaniya na kasar wanda zai kakkabo jiragen yake samfurin jet mafi inganci a wajen makiya daga sararin samaniyar kasar.

Yakin kwanaki 12 dai ya zama kamar gwaji ne ga ingancin makamai da kuma garkuwan sararin samania na kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments