Dakarun sojin kasar iran sun kaddamar da hare hare da makami mai linzami da jirgin sama mara matuki kan sansanonin sojin Amurka dake kasashen Jodan Kuwait da kuma kasar bahrain, da kuma Oman a matsayin martani kan harin da Amurka ta kai a kudancin iran, kuma rundunar tsaro ta kare juyin musulunci na iran suka yi gargadin cewa duk wani mataki da Amurka ta dauka zai fuskanci mummunan martani.
a cikin wani bayani da bangaren hulda da jama’a na dakarun kare juyin musulunci ya fitar ya ce Amurka ta yi kokarin sake gwada abin da ta gwada a baya ta hanyar tilastawa gwamnatin Oman da kuma haifar da fitna akan hanyar da ya sabama doka inda jirage da dama za su wuce ta kudancin mashigar Hurmuz a matsayin wani gwaji da ta riga tayi irinsa a baya.
haka zalika bayanin ya ci gaba da cewa kasar Amuka ta kaddamar da hari kan wasu sansanoni da bangaren sadarwa a kudancin kasar iran , sai dai dakarun kare juyin musulunci sun kai hari kan sansanin soja Amurka mafi muhimmanci dake jodan,
daga karshe dakarun sojin na iran sun yi gargadin cewa Amurka da isra’ila ne ke da alhakin tashin hankali, kuma za su fuskanci mayar da martani mai tsanani idan ta sake kai mata hari , cibiyar sojin Amurka ta bayyana cewa ta kai harin ne bisa umarnin shugaban Amurka Donald Trump da niyar rage karfin ikon iran a mashiyar Hurmuz.