Iran Ta Jajantawa Koriya Ta Kudu Da Thailand Kan Hatsarin Jirgin Sama

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghaei, ya jajanta wa Koriya ta Kudu bayan wani hadarin jirgin sama da ya yi sanadin mutuwar mutane da

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghaei, ya jajanta wa Koriya ta Kudu bayan wani hadarin jirgin sama da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Baghaei ya mika sakon ta’aziyyar Iran da jaje ga gwamnati da al’ummar Koriya ta Kudu da Thailand, musamman ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, yana mai fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a wannan mummunan lamari.

Da sanyin safiyar yau ne, wani jirgin saman fasinja na Koriya ta Kudu ya kama wuta bayan da ya zarce daga titin saukar jiragen sama a filin jirgin saman kasa da kasa na garin Muan.

Hukumomin Koriya ta Kudu sun ce mutane 181 na cikin jirgin fasinja na Jeju Air da ke dawowa daga Bangkok babban birnin kasar Thailand.

Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane sama da 150.

Jirgin saman fasinja ya kone kurmus bayan ya afkawa wani shingen kankare lokacin da na’urar fitar tawowinsa suka makkale, kamar yadda jami’ai suka ce, a daya daga cikin mafi munin jirgin saman kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments