Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Azeri Ilham Aliyev yau Alhamis bayan wani mummunan hatsarin jirgin sama da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 38 a cikinsa.
A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Pezeshkian ya jajanta wa shugaban kasar Azabaijan da iyalan wadanda abin ya shafa, yana mai fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Shugaban na Iran ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen fadada alakarta da Jamhuriyar Azarbaijan kafin ya gayyaci Aliyev zuwa birnin Tehran.
Jirgin na AZAL wanda ya taso daga Baku zuwa Grozny ya yi hatsari a kusa da birnin Aktau ranar Laraba.
Daga cikin mutane 67 da ke cikin jirgin, 38 sun rasa rayukansu, yayin da 29 suka tsira.