Kasar Iran ta jaddada cewa: Ba za ta yi watsi da haƙƙinta ba saboda matsin lamba na siyasa
Kakakin hukumar makamashin nukiliya ta Iran, Behrouz Kamalvandi ya mayar da martani kan matakin siyasa na rashin dacewa da kwamitin alkalan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya dauka kan kasar Iran da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta yi watsi da haƙƙinta da dokokin kasa da kasa suka tabbatar mata ba saboda fuskantar matsin lamba na siyasa, kuma ya bukaci kasashen yammacin duniya da su dauki hanyar mu’amala ta kwarai da karfin gwiwa.
Behrouz Kamalvandi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labaran Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yammacin jiya Laraba dangane da martanin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mayar kan matakin da kasashen yammacin duniya suka dauka a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya. Kamar yadda ya jaddada cewa: Fitar da kudurinsu mataki ne maras amfani. Ya kara da cewa: Daga yau Iran ta fara aiwatar da tsare-tsare na kare manufofinta kuma tana sa ran kasashen yammacin duniya za su zabi hanyar mu’amala da hadin kai da suka dace a maimakon yin amfani da kungiyoyin kasa da kasa wajen daukan matakin matsin lamba, sannan lallai Iran ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare haƙƙoƙinta tare da kalubalantar duk wani matsin lamba na siyasa.