Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana tir da allawadai da hare-haren da sojojin Amurka suka kai kasar Venezuela a jiya Asabar sannan ya ce gwamnatin kasar Iran tana goyon bayan mutanen kasar Venezuela da gwamnatinsu.
A wata hira tsakaninsa da tokwaransa na kasar Venezuela Yyan Gil Pinto a daren Asabar Argchi yace sun tattauna irin halin da kasar Venezuela take ciki da kuma hare-haren kasar Amurka a kan kasar. Ya ce hare-haren aikin ta’addancin ne na kasa da kasa a fili kuma shugaban Madoro shi ne halitaccen shugaban kasar wanda mutane suka zaba.
A nashi bangaren Yyan Gil Pinto yace mutanen kasar Venezuela tare da duk abinda ya faru, a shirye suke su kare kasarsu daga mamayar wata kasa, da kuma tabbatar da yencinta.
Sun yi Allawadai da fin karfin da Amurka ta nunawa kasar, har ta sace shugaban kasa da matarsa. Bayan kama shi dai Amurkawan sun kaishi birnin NewYork suka tsare inda suka