Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran wato Iran Space Agency (ISA) ya gwada wani kumbo mai daukan taurari zuwa sama mai sunan Qadir tare da nasara.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a wannan karon kumbo mai dauka taurarin ko Qadir bai dauke da kome zuwa sararin samania saboda ana gwada shi ne.
ISA ta tabbatar da ingancin kumbo bayan wannan gwajin, sannan iran zata iya amfani da wannan Kombon don aika taurari zuwa sararin samani da shi ba tare da fuskantar wata matsala nan gaba.