Iran Ta godewa Rasha Dangane Goyon bayanta Kan Hakkinta Na Tace Yuranium

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya godewa kasar Rasha saboda goyon bayanta ga kasar kan hakkinta na tace makamashin uranium, musamman a taron kwamitin tsaron

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya godewa kasar Rasha saboda goyon bayanta ga kasar kan hakkinta na tace makamashin uranium, musamman a taron kwamitin tsaron MDD wanda za’a gudanar nan gaba dangane da kudurin kwamatin mai lamba 2231 dangane shirin nukiyar kasar Iran ta JCPOA, Inda kasashen turai 3 wato triko wadanda suke bukatar sake dawoda takunkuman MDD kan kasar ta Iran.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakato Pezeshkiyan yana fadar haka a lokacinda yake magana ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putun a yau litinin.

A nashi bangaren shugaba Putin ya bayyana cewa Rasha za ta tabbatar da cewa sakamakon taron kwamitin tsaro dangane da shirin “snapback” zai fito mai kyau ga kasar Iran. Ya ce Rasha tana goyon bayan Iran kan hakkinta na tace makamacin Uranium.

Shuwagabannin sun tattauna wasu al-amura da suka shafi shinfida ayin dogo na Rash Stana, da kuma titin hada arewa da kudu, da kuma taron Putin da Trump a Alaska. Inda shugaban kasar Iran yani fatan taron ya kasance mai amfani don kawo karshen yaki a Ukraune.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments